Kimanin ƴan Najeriya dubu 3 da 270 sun samu takardun zama ƴan Amurka sakamakon shiga aikin sojin ƙasar a baya-bayan nan. Najeriya ce ta huɗu a jerin ƴan ƙasashen da Amurka ta ba su takardun zama ƴan ƙasa ta hanyar hidinmta mata a ɓangaren aikin soji tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024.
A jumulce, Amurka ta bai wa ƴan ƙasashen ƙetare kimanin dubu 52 takardun zama ƴan ƙasa a ƙarkashin aikinsu na soji a ƙasar. Alkaluman da hukumar kula da takardun Ƴan Ƙasa da Shige da Fice ta Amurka ta fitar a wannan Litinin, sun nuna cewa, ƴan asalin ƙasar Philippines dubu 5 da 630 ne suka samu takardun zama ƴan Amurka a ƙarƙashin aikin sojin, sai Jamaica da ke biye mata a matsayi na biyu, inda take da dubu 5 da 420, yayin da Mexico ke a matsayi na uku, inda take da dubu 3 da 670.
Sai kuma Najeriya da ta zo ta biyar da adadin mutum dubu 3 da 270 da suka shiga aikin sojin tare da samun takardun zama ƴan Amurka. Sauran ƙasashen sun haɗa da Ghana da Haiti da China da Kamaru da Vietnam da Koriya ta Kudu kamar yadda alkaluman hukumomin Amurka suka nuna. Alkaluman sun nuna cewa, adadin ƴan Najeriya da ke shiga aikin soji a Amurka na ci gaba da karuwa a kai a kai cikin shekaru biyar da suka gabata.
Malaysia Latest News, Malaysia Headlines
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunciShugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa “mugayen” ‘yan Najeriya za su fuskanci hukunci kamar doka ta tanada. Tinubu ya gargadi masu aikata mugayen laifuka, ko suna cikin Najeriya ko waje, cewa za a gurfanar da su gaban shari’a.
Read more »
Tinubu ya jagoranci manyan ‘Yan Najeriya a Addu’o’in Fidau na Sheikh BelloShugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya jagoranci manyan 'yan Najeriya wajen halartar addu'o'in Fidau na kwana uku domin sheikh, Muhydeen Bello, wanda ya Tinubu ya jagoranci manyan 'Yan Najeriya a Addu'o'in Fidau na Sheikh Bello
Read more »
Yan Najeriya 10,000 aka samu da karya ka’idar shige da fice a bana -Kashim ShettimaMataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa akalla ‘yan Najeriya 10,000 ne aka tsare bisa laifukan karya dokokin shige da fice a kasashen Afirka da kasashen Turai a bana.
Read more »
Yan sandan sun cafke mutanen da ake zargi da safarar Dalolin bogi zuwa KanoRundunar yan Sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama miliyoyin Dalolin kasar Amurka da Naira da kuma sauran kudaden ketare, da Ake zargin na bogi ne don cutar da ƴan kasuwa.
Read more »
Gwamna Sani ya ba yan kwangila makonni 6 su kammala aikin titin KadunaGwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ba wa 'yan kwangilar da ke gudanar da aikin titin Ungwan Rimi-Kafanchan a cikin garin Ƙafanchan, karamar hukumar Jema’a ta jihar, wa’adin makonni shida su kammala aikin.
Read more »
Kungiyar tsofaffin yan sanda ta yi barazanar yajin aikin cin abinciKungiyar tsofaffin ‘yan sandan Najeriya (NUP), reshen jihar Kano, ta yi barazanar fara yajin aikin cin abinci. Kungiyar ta ce za ta dauki matakin ne domin matsawa gwamnatin tarayya da hukumar kula da fanshon ‘yan sanda su biya su hakkokinsu.
Read more »