Jinkirin Jirage: Najeriya za ta hukunta kamfanonin jiragen sama masu laifi

Jiragen Sama News

Jinkirin Jirage: Najeriya za ta hukunta kamfanonin jiragen sama masu laifi
NcaaNCAA DG
  • 📰 DailyPostNGR
  • ⏱ Reading Time:
  • 26 sec. here
  • 4 min. at publisher
  • 📊 Quality Score:
  • News: 21%
  • Publisher: 59%

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama, NCAA ta bayyana aniyarta na daukar matakin ladabtarwa kan kamfanonin jiragen sama da ke jinkirin tashi ba tare da gamsassun dalilai ba.

Haka kuma, ta yi kira ga Fasinjoji su kara samun fahimtar kalubalen da za su iya fuskanta yayin tafiye-tafiye ta filayen jiragen sama . Shugaban Sashen Kare Hakkin Fasinjoji na Hukumar NCAA , Michael Achimugu, ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani tattaki da aka gudanar a birnin Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Ya ce wannan lokaci ne na yawan tafiye-tafiye, don haka akwai bukatar wayar da kan matafiya yadda ya kamata kan dalilan jinkiri da hanyoyin magance matsalolin.

Achimugu ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da ake yawan tafiye-tafiye ta jiragen sama, kuma ana fuskantar matsaloli da dama kamar jinkiri da rushewar jadawalin jirage, wanda ya haifar da korafe-korafe daga fasinjoji. Ya ce aikin NCAA shi ne wayar da kan fasinjoji, domin sau da yawa matsalolin da ake samu na biyo baya ne daga rashin sanin hakkoki da nauyin da ke kansu a matsayin matafiya ta jiragen sama. “Dole ne mu kare hakkin fasinja da kuma martabar kamfanonin jiragen sama,” in ji Achimugu.

We have summarized this news so that you can read it quickly. If you are interested in the news, you can read the full text here. Read more:

DailyPostNGR /  🏆 11. in NG

Ncaa NCAA DG

Malaysia Latest News, Malaysia Headlines

Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.

IHRC ta zargi CBN da nuna wariya ga ma’aikatan masu alaka gwamnatin BuhariKungiyar kare hakkin Dan adam ta Duniya wato International Human Rights Commission (IHRC), zargi Babban Bankin Najeriya (CBN) da nuna bambanci tsakanin ma’aikata. Babban Daraktan Kungiyar na Najeriya, Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa ga manema labarai a Kano.
Read more »

Rahoton mutuwar mutum 10,000 a hannun sojoji: Najeriya ta gayyaci Amnesty Int’lShalkwatar tsaro ta kasa ta gayyaci kungiya kare hakkin dan Adam ta Amnesty International domin gabatar da hujjojin ta  kan zargin da ta yi na cewa mutane 10,000 sun mutu yayin da suke tsare a hannun sojoji tun bayan fara yakin Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Read more »

Babu sansanin sojin wata kasa a Najeriya – Janar Christopher MusaShugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ya musanta rahotannin da ke cewa an baiwa Faransa izinin kafa sansanin soji a Najeriya.
Read more »

Gwamnati ta musanta bullar sabon nau’in cutar COVID-19 a NajeriyaMa'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta bullar sabon nau'in cutar COVID-19 mai suna XEC a Najeriya.
Read more »

Tsofaffin Sojoji sun fara karɓar hakkokinsu bayan zanga-zangaGwamnatin Tarayya ta fara biyan hakkokin tsofaffin sojojin Najeriya a ranar Juma’a, bayan dogon lokaci suna jiran kudaden da aka amince da su. Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffin sojojin suna dade suna samun uzuri na rashin kuɗi duk da amincewa da biyan kudaden.
Read more »

Gwamnati ta gargadi asibitoci su kwana da shirin sabuwar cutar COVID-19Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi ga asibitocin kasar nan da sauran cibiyoyin lafiya su kasance cikin shiri kan sabon nau'in cutar COVID-19 na XEC, dake cigaba da bazuwa cikin sauri.
Read more »



Render Time: 2025-03-13 16:32:45